Home Labaru An Tsige Mataimakin Shugaban Majalisar Dokoki Ta Jihar Taraba

An Tsige Mataimakin Shugaban Majalisar Dokoki Ta Jihar Taraba

407
0

‘Yan majalisar dokoki ta jihar Taraba, sun tsige mataimakin shugaban majalisar Mohammed Gwampo.

Wata majiya ta ce, an tsige dan majalisa Gwampo ne a zauren majalisar ranar Litinin, 7 ga watan Oktoba na shekara ta 2019.

Gwampo dai ya kasance dan majalisa mai wakiltar mazabar Yorro a majalisar dokoki ta jihar Taraba.