Home Labaru Tsaro: Mun Samu Gagarumar Nasara Wajen Dagargaza Boko Haram – Buhari

Tsaro: Mun Samu Gagarumar Nasara Wajen Dagargaza Boko Haram – Buhari

258
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya Nijeriya ta samu gagarumar nasara wajen rage karfin ‘yan ta’addan Boko Haram.

Buhari ya yi ikirarin ne, yayin kaddamar da wasu jami’an sojin sama a matsayin matukan jirgin sama a sansanin helkwatar rundunar da ke Kaduna.

Shugaban Buhari, wanda ya samu wakilcin Shugaban ma’aikatan tsaro Abayomi Olonisakin, ya ce an sanya wadanda ke yunkurin tarwatsa Nijeriya cikin mawuyacin hali.

Haka kuma, shugaba Buhari ya bukaci sabbin jami’an da aka kaddamar su fuskanci makiyan Nijeriya, tare da yin amfani da sabbin dabaru.

Ya ce a shekaru hudu da su ka gabata, rundunar sojin sama ta gyara jiragen da su ka lalace ta kuma shigo da sababbi, lamarin da ya sa ta iya cimma bukatun gwamnati da jin dadin da jami’an ta ke bukata.