Home Labaru Ilimi An Kulle Makarantar Mata Ta Gwamnati Da Ke Dapchi A Jihar Yobe

An Kulle Makarantar Mata Ta Gwamnati Da Ke Dapchi A Jihar Yobe

825
0

Kungiyar malamai da iyayen baliban makarantar Dapchi da kungiyar yaran makarantar da aka sace, sun yanke shawarar kulle makarantar sakandaren mata zalla da ke Dapci jihar Yobe saboda gudun kada tarihi ya maimaita kan sa.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 19 ga watan Febrairu na shekara ta 2018 ne, mayakan Boko Haram su ka sace ‘yan mata 104 daga makarantar.

Wata Majiya ta ce kungiyoyin sun yanke shawarar kulle makarantar ne bisa wani rahoton tsaro da aka ba su har sau uku.

Shugaban kungiyar iyayen daliban Bashir Manzo, ya ce kwamandan rundunar tsaro ta JTF na garin, ya basu umurnin kwashe yaran su daga makarantar zuwa gidan sarki. Ya ce sun yi ittifaki wajen yanke shawarar, saboda rahoton leken asiri da aka samu ranar Asabar da ta gabata, cewa an ga ‘yan ta’addan a kauyen Sassawa, shi ya sa hukumar makarantar ta gana da kungiyar malamai da iyaye da jami’an tsaro, kuma sun amince a kulle makarantar.