Kungiyar Amnesty International a Nijeriya, ta yi watsi da matsayin da ministan watsa labarai Lai Mohammed ya ɗauka na cewa ba a samu kashe-kashe a zanga-zangar EndSARS da ta faru a Legas ba.
Haka kuma, kungiyar marubuta a kan harkokin kare hakkin bil’adama ta Nijeriya HURRIWA, ta soki lamirin ministan da cewa ba ta san zaman da ya key i a kan kujerar ministan yada labarai a Nijeriya ba.
Kungiyoyin sun ce, yadda ake samun jawaban shugaban kasa da ministan yada labarai suna karo da juna a kan matsayar gwamnati game da lamari mai muhimmanci, hakan zai iya sauya tunanin ‘yan Nijeriya su ki gaskanta duk abin da gwamnati za ta fada nan gaba.
You must log in to post a comment.