Home Labaru Saraki Ya Ziyarci Jihar Benue A Kan Kudirin Sa Na Takarar Shugaban...

Saraki Ya Ziyarci Jihar Benue A Kan Kudirin Sa Na Takarar Shugaban Kasa

42
0

Tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata Abubakar Bukola Saraki, ya ziyarci Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue a kan kudirin sa na tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a zaben shekara ta 2023.

Bukola Saraki, wanda ya yi ganawar sirri da gwamna Ortom ya kuma gana da kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a jihar domin sanar da su kudirin sa na fara tuntuba game da aniyar sa ta takarar shugaban kasa.

Ya ce sauya shekar da masu biyayya ga jam’iyyar APC ke yi zuwa PDP a fadin Nijeriya, alamu ne da ke nuna cewa jam’iyyar na iya zama babu kowa a cikin ta kafin zabe mai zuwa.

Bukola Saraki, ya ce yankin arewa ta tsakiya ya sauke nauyin shi ta hanyar aiki tukuru, domin ganin dorewar hadin kan Nijeriya a matsayin tsintsiya madaurin ki daya.