Home Labaru Gwamna Zulum Ya Kaddamar Da Manyan Ayyuka 23 A Kudancin Borno

Gwamna Zulum Ya Kaddamar Da Manyan Ayyuka 23 A Kudancin Borno

61
0

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da ayyuka 23 a kudancin jihar, wadanda su ka hada da makarantu da asibitoci a wasu kauyuka da garuruwa.

Mai magana da yawun gwamnan Malam Isa Gusau, ya ce Zulum ya kaddamar da ayyuka 23 daga cikin sauran ayyukan da gwamnatin ta aiwatar a kudancin jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar Borno ta wallafa a shafin ta na Facebook, ta ce ayyukan sun hada da sabbin makarantun sakandare da firamare 13 da aka gina da kuma gyara su.

Sauran sun hada da da cibiyoyin kula da lafiya matakin farko guda shida, da gine-ginen kananan hukumomi uku da su ka hada da ofisoshin ‘yan sanda biyu da gidan gwamnati da kuma rukunin shaguna.