Home Labaru Rimingado: Rudani A Kano Bayan Majalisar Jiha Ta Gayyaci Shugaban Alkalai

Rimingado: Rudani A Kano Bayan Majalisar Jiha Ta Gayyaci Shugaban Alkalai

87
0

Wasikar gayyatar da majalisar dokoki ta jihar Kano ta aike wa shugaban alkalan jihar mai shari’a Nura Sagir Umar ta haddasa dimuwa a jihar Kano.

A cikin wasikar da daraktan shari’a Nasidi Aliyu ya sanya wa hannu, ya bukaci shugaban alkalan SU bayyana a gaban kwamitin majalisar a ranar 28 ga watan Yuli.

Wata majiya ta ce, an aikA da wasikar gayyatar ne saboda wani umarnin kotu da Mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya bada, na hana ci-gaba da binciken dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa na jihar Kano Muhuyi Magaji Rimingado.

Sai dai wata majiyar ta ce, shugaban alkalan ya ki amsa gayyatar, kuma bai yi martani ba balle ya bayyana a gaban kwamitin.

Mai magana da yawun fannin shari’a na jihar Baba Jibo Ibrahim ya shaida wa manema labarai cewa, sun yanke hukuncin mika lamarin ga kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Kano saboda ba su son hada al’amurra da mahukunta.

Yayin da aka tuntubi shugaban kungiyar Lauyoyi ta jihar Kano Aminu Gadanya, ya ce shugaban alkalan ya yi daidai da bai bayyana a gaban kwamitin majalisar ba.