Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Ambaliya: Ganduje Ya Gwangwaje Iyalan Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa Da Tallafin Kudi

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya bada tallafin Naira dubu 200 ga kowanne daga cikin iyalan mutane 18 da ambaliyar ruwa ta kashe a Doguwa.

Ganduje dai ya kai ziyarar musamman ne domin ta’aziyya ga iyalan mamatan, inda ya yi addu’ar samun rahama ga waɗanda su ka rasu sanadiyyar ruwan sama mai tsanani.

Ya ce a lokacin da su ka samu labarin sun kaɗu sosai, don haka su na addu’ar Allah ya gafarta ma waɗanda ruwan ya tafi da rayuwar su.

Exit mobile version