Home Labaru Kiwon Lafiya Alkalumma: An Samu Karin Mutane 20 Da Suka Kamu Da Coronavirus, Jimilla...

Alkalumma: An Samu Karin Mutane 20 Da Suka Kamu Da Coronavirus, Jimilla 343

284
0

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta ce. an samu karin mutane 20 da suka kamu da cutar Coronavirus a Nijeriya.

Rahoton cibiyar na ranar  Litinin, 13 ga Afrilu wanda ta wallafa a shafin Tuwita ya ce, an samu karin mutane 20 da su ka kamu da cutar,  inda jihar Legas ke da 13,  2 a jihohin Edo da Kano da kuma Ogun, sai guda a jihar Ondo.

Alkalummar cibiyar sun tabbatar da cewa, yanzu nijeriya ta na da  mutane 343 suka kamu da cutar a Nijeriya, sai dai 91 sun warke, kana 10 sun mutu, wanda hakan ya tabbatar da mutane 242  da ke cikin jinyar cutar yanzu haka a fadin Nijeriya.