Cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta ce. an samu karin mutane 20 da suka kamu da cutar Coronavirus a Nijeriya.
Rahoton cibiyar na ranar Litinin, 13 ga Afrilu wanda ta wallafa a shafin Tuwita ya ce, an samu karin mutane 20 da su ka kamu da cutar, inda jihar Legas ke da 13, 2 a jihohin Edo da Kano da kuma Ogun, sai guda a jihar Ondo.
Alkalummar cibiyar sun tabbatar da cewa, yanzu nijeriya ta na da mutane 343 suka kamu da cutar a Nijeriya, sai dai 91 sun warke, kana 10 sun mutu, wanda hakan ya tabbatar da mutane 242 da ke cikin jinyar cutar yanzu haka a fadin Nijeriya.














































