Home Labaru Kiwon Lafiya Kawar Da Corona: Gwamna Fayemi Ya Tsawaita Dokar Hana Fita Na Makonni...

Kawar Da Corona: Gwamna Fayemi Ya Tsawaita Dokar Hana Fita Na Makonni Biyu

230
0

Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya kara wa’adin dokar hana fita zuwa makonni 2 domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a fadin jihar.

Fayemi ya bayyaba haka ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Biodun Oyebanji ya sa hannu a ranar litinin din da ta gabata.

Sai dai gwamna Fayemi ya ce za a kyule mutane su gudanar da harkokin su na yau da kullum da misalin karfe 6 na safe zuwa 2  na rana, : domin su samu damar sayen kayan abinci a kasuwa.

Haka kuma, daga ranar Talatar nan ya zama wajibi kowa ya rika amfani da tsummar rufe fuska, wanda hakan zai zai taimaka wajen rage yaduwar wannan a jihar, tare da cewa za a samar da takunkumin rufe fuska ga ma’aikatan da aka ba damar fita zuwa wajen aiki.

A karshe gwamana Fayemi ya ce, gwamnatin sa za ta cigaba da koyar da daliban makarantun Firamare da Sakandare a kafar yanar gizo, saboda dabbaka dokar hana cinkoson mutane a waje guda.

Idan dai ba a manta ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara wa’adin dokar hana shiga da fita a jihohin Legas da Ogun da kuma babban birnin tarayya Abuja.