Home Labaru Kiwon Lafiya Alkalumman Kano: An Samu Karin Mutane Biyu Da Suka Kamu Da...

Alkalumman Kano: An Samu Karin Mutane Biyu Da Suka Kamu Da Coronavirus

365
0

Gwamnatin Kano ta ce an samu karin mutane biyu da suka kamu da cutar coronavirus, kwana biyu da bullar cutar a jihar.

Mai taimakawa wamna Abdullahi Ganduje kan harkokin yada labarai Salihu Tanko Yakassai ya bayyana haka a yammacin Litinin din da ta gabata, tare da cewa yanzu jihar na da adadin mutanen uku da suka kamu da cutar.

Yakasai ya kara da cewa, an sake samun karin mutum 2 da suka kamu da cutar ne bayan sakamakon gwajin da aka yi musu, wanda ya tabbatar da cewa su na dauke da cutar.

Idan dai ba a manta ba, a ranar Asabar ne aka sanar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar, bayan  mutumin ya yi tafiya daga Legas zuwa Abuja sannan ya iso jihar Kano.