Home Coronavirus Albashi: Sai Da Lambar Bvn Za Ku Samu Albashin Ku – Gwamnati

Albashi: Sai Da Lambar Bvn Za Ku Samu Albashin Ku – Gwamnati

447
0
Albashi: Sai Da Lambar Bvn Za Ku Samu Albashin Ku - Gwamnati
Albashi: Sai Da Lambar Bvn Za Ku Samu Albashin Ku - Gwamnati

Gwamnati tarayya ta ce sai da lambar BVN ‘ya’yan kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU za ta samu albashin su na  watannin biyu.

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yaki da annobar da COVID-19.

Boss Mustapha ya kara da cewa, bisa tausayi irin na shugaban kasa Buhari ya bada umurnin a biya malaman jami’o’i  albashin su bisa shadadin sai shugabannin jami’o’i sun mallaki lambar BVN.

Sai dai shugaban kungiyar Biodun Ogunyemi, ya ja kunnan daukacin malaman jami’o’in kada su kuskura su bada lambar BVN.

Ogunyemi ya kara da cewa, sun godewa shugaban kasa Buhari da bisa umarnin da ya bada na biyan su albashin su, duk da cewa tun farko bai kamata ma ya rike mana albashin su na watannin Febreru da Maris ba.

Haka kuma, shugaban kungiyar ASUU ya ce ba su amince da sharadin cewa sai da lambar BVN kafin a biya su albashin su ba, sakamakon suna tunanin ana kokarin sa su cikin shirin biyan albashin na IPPIS a fakaice.