Home Labaru Faduwar Farashin Mai: Atiku Ya Bada Shawara

Faduwar Farashin Mai: Atiku Ya Bada Shawara

450
0
Faduwar Farashin Mai: Atiku Ya Bada Shawara
Faduwar Farashin Mai: Atiku Ya Bada Shawara

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bada shawarar matakan da za abi wajen dai-dai-ta tattalin arzikin Nijeriya, a wannan lokaci da annobar COVID-19 ta addabi duniya.

Atiku Abubakar

Atiku ya ce, kasuwar man fetur a duniya na ci gaba da samun koma-baya sakamakon bullar annobar Coronavirus, saboda haka lokaci ya yi da za a samar da kariya mai dorewa ga tattalin arzikin kasa.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa, wajibi ne Nijeriya ta kafa ma’adanar danyen man fetur mai matukar rinjaye a duniya, wanda hakan zai sa a siyar da man a lokacin  ya fadi warwas.

Atiku ya ce Amurka ta Arewa da kasashen Turai duk suna da hanyoyin da suke bi domin bada kariya ga dukkan bangarori na tattalin arzikin su, saboda haka bai kamata a bar Nijeriya a baya ba.

Haka kuma, Atiku Abubakar ya kara da bada shawarar cewa, akwai bukatar Nijeriya ta tattauna da abokan huldar ta masu fitar da danyen man fetur domin samun matsaya, wanda hakan ne zai bada dama wajen shawo kan matsalar faduwar farashin man fetur da kuma samar da dai-dai-to a tattalin arzikin Nijeriya.