Home Labaru Covid-19: Gwamnoni Sun Amince Da Dokar Rufe Jihohin Nijeriya Na Tsawon Kwanaki...

Covid-19: Gwamnoni Sun Amince Da Dokar Rufe Jihohin Nijeriya Na Tsawon Kwanaki 14

526
0
Covid-19: Gwamnoni Sun Amince Da Dokar Rufe Jihohin Nijeriya Na Tsawon Kwanaki 14
Covid-19: Gwamnoni Sun Amince Da Dokar Rufe Jihohin Nijeriya Na Tsawon Kwanaki 14

Kungiyar Gwamonin Nijeriya ta amince da kafa dokar kulle daukacin jihohin Nijeriya 36 na tsawon makonni biyu a wani matakai na dakile yaduwar Coronavirus.

Gwamnonin sun cimma wannan matsaya ne bayan sun saurari bayanai daga gwamnonin jihohin Lagos da Bauchi da Oyo da Ogun a kan darussan da su ka koya daga a annobar COVID-19.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya sanar da haka jim kadan bayan kammala taron kungiyar da ya gudana ta hanyar amfani da yanar gizo.

Gwamnoni sun kuma bukaci gwamnatin tarayya ta rage nauyin alhakin duba yaduwar annobar covid-19 daga wuyanta tare da dora shi a wuyan jihohi, saboda yadda cutar ta yadu zuwa jihohi fiye da 25.

Haka kuma, gwamnonin sun nuna damuwar su a kan yadda cutar COVID-19 ke kama likitoci da sauran ma’aikatan lafiya, yayin da su ke aikin ceton rayuwar wadanda su ka kamu da r cutar.

Gwamnonin su ce za su hada gwuiwa da cibiyar dakile cututtuka ta kasa NCDC wajen horar ma’aikatan lafiya a kan hanyoyin da za su kare kan su a lokacin da su ke duna lafiyar wadan da suka kamu da cutar, da kuma samar masu da wadatattun kayan aiki.

Leave a Reply