Home Labaru Kiwo: Ganduje Ya Yi Kira Ga Gwamanati Ta Hana Fulani Shiga Kudanci

Kiwo: Ganduje Ya Yi Kira Ga Gwamanati Ta Hana Fulani Shiga Kudanci

262
0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bukaci gwamnatin tarayya ta dakatar da tashin da makiyaya ke yi daga Arewacin Najeriya zuwa Kudanci domin magance rikicin manoma da makiyaya.

Ya ce shirin samar da wuraren zama na zamani ga makiyaya shine mafita ga yawan rikice-rikice da ake samu a tsakanin manoma da makiyayan.

Ganduje, ya ce samawa Fulanin matsuguni a jihar ya zama wajibi, domin abu ne mai kyau kuma gwamnatinsa ta rungumi shirin hannu bibbiyu. Ya ce akwai matakai da dama da gwamnatin jihar za ta dauka wajen samar da matsugunan na makiyaya ta yadda jihar zata amfana ta bangarori da dama