Tsohon dan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani, ya soki lamirin shugaba Buhari a kan tura wakilan musamman zuwa Afrika ta Kudu game da hare-haren da ake kai wa ‘yan Nijeriya da shagunan su a kasar.
Sanata Shehu Sani, ya wallafa a shafin san a twitter cewa, ba daidai ba ne gwamnatin tarayya ta tura wata tawagar musamman zuwa ga gwamnatin kasar Afrika ta Kudu.
Ya ce kamata ya yi a ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika wakilai zuwa ga iyalan wadanda lamarin ya shafa maimaikon tura wakilai zuwa kasar Afrika ta Kudu.
Idan dai za a iya tunawa, Shugaba Muhammadu Buhari ya tura tawaga zuwa kasar Afirka ta kudu, domin ganawa da shugaban kasar Cyril Ramaphosa.