Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya ba shi tallafi na kimanin naira biliyan 30 da miliyan 8 domin biyan bashin albashin ma’aikatan jihar.
Yahaya Bello dage a kan cewa a halin yanzu ba a bin gwamnatin sa bashin albashi domin ta na biyan ma’aikata duk wata.
Gwamnan ya bayyana wa manema labarai haka ne, bayan ganawar da ya yi da kwamitin Jam’iyyar APC na kasa, da wadanda su ka yi takarar zaben fidda gwani na kujerar gwamnan jihar Kogi a zabe mai zuwa.
Dangane da labaran da ake yadawa cewa ma’aikata na bin jihar Kogi bashin albashi, ya ce matsala ce da ya gada a lokacin da ya hau mulki, amma a halin yanzu ma’aikata basu bin jihar Kogi bashin albashi.