Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Afrika Ta Kudu: Sanata Shehu Sani Ya Soki Lamirin Gwamnatin Tarayya

Sanata Shehu Sani, Tsohon Dan Majalisar Dattawa

Sanata Shehu Sani, Tsohon Dan Majalisar Dattawa

Tsohon dan majalisar dattawa Sanata Shehu Sani, ya soki lamirin shugaba Buhari a kan tura wakilan musamman zuwa Afrika ta Kudu game da hare-haren da ake kai wa ‘yan Nijeriya da shagunan su a kasar.

Sanata Shehu Sani, ya wallafa a shafin san a twitter cewa, ba daidai ba ne gwamnatin tarayya ta tura wata tawagar musamman zuwa ga gwamnatin kasar Afrika ta Kudu.

Ya ce kamata ya yi a ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika wakilai zuwa ga iyalan wadanda lamarin ya shafa maimaikon tura wakilai zuwa kasar Afrika ta Kudu.

Idan dai za a iya tunawa, Shugaba Muhammadu Buhari ya tura tawaga zuwa kasar Afirka ta kudu, domin ganawa da shugaban kasar Cyril Ramaphosa.

Exit mobile version