Home Labaru Ramuwar-Gayya: Za A Hukunta Wadanda Su Ka Kai Hari Kan Kamfanonin Afirka...

Ramuwar-Gayya: Za A Hukunta Wadanda Su Ka Kai Hari Kan Kamfanonin Afirka Ta Kudu

186
0
Mohammed Adamu, Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya
Mohammed Adamu, Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya

Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu, ya ce ‘yan Nijeriya 36 ne aka kama da laifin watanda da dukiyar ‘yan kasar Afirka ta Kudu da sunan ramuwar-gayya.

Mohammed Adamu ya bayyana wa manema labarai haka ne, yayin wata ziyara da su ka kai ma shi a ofishin hukumar ‘yan sanda da ke Ado Ekiti.

Adamu ya ce Nijeriya kasa ce da aka gina da dokoki, kuma duk wanda aka kama da laifin nuna bambanci ga ‘yan wata kasa mazauna nan za a kama shi da laifin ta’addanci da rashin kishin kasa.

Ya ce kamen an yi shi ne domin bin doka da kuma adalci, sanna a nuna wa duniya cewa ‘yan Nijeriya su na bin doka, don haka ba za su yi yadda wasu kasashen ke yi ba.

Ya ce gwamnatin tarayya ta na yin abin da ya dace a kan harin da ake kai wa ‘yan Nijeriya a kasar Afirka ta Kudu, don haka wannan ba zai bada lasisin kai hari a kan dukiyoyin ‘yan Afirka ta kudu ko wata kasa ba.