Annobar coronavirus ta yi sanadiyyar mutuwar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasar Najeriya, Abba Kyari.
A tsakar daren Juma’a 17 ga Afrilun 2020 ne Abba Kyari ya rasu a inda ake jinyarsa bayan kamuwarsa da cutar coronavirus.
An ci gaba da jinyar Abba Kyari a Legas ne bayan ya yanke shawarar komawa Legas daga Abuja, inda ya dauki nauyin kula da lafiyarsa daga aljihunsa.
Kakakin Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu ya sanar da haka a cikin sakon da ya fitar ta shafinsa na Twitter.
Abba Kyari shi ne mutum mafi girman matsayi da cutar COVID-19 ta fara kamawa a Najeriya. Kana kuma a kansa aka fara samun bullar cutar a fadar shugaban kasar.
An gano yana dauke da cutar ne bayan dawowarsa daga kasashen waje.
Kamuwarsa da cutar ta haifar da fargabar yaduwar COVID-19 a tsakanin gwamnoni da wasu manyan jami’an gwamnati da suka yi hulda da shi kafin bayyanr cutar tasa. Hakan ta sa wasu daga cikinsu killace kansu.
You must log in to post a comment.