Home Labaru Kiwon Lafiya Coronavirus: An Samu Karin Mutum 35 A Nijeriya, Jimmila 442

Coronavirus: An Samu Karin Mutum 35 A Nijeriya, Jimmila 442

604
0
Coronavirus: An Samu Karin Mutum 35 A Nijeriya, Jimmila 442
Coronavirus: An Samu Karin Mutum 35 A Nijeriya, Jimmila 442

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta tabbatar da samun karin mutum 35 da suka kamu da cutar COVID-19 Nijeriya.

Alkalumman cibiyar sun nuna cewa, yanzu haka akwai jimillar mutane 442 da suka kamu cutar a fadin Nijeriya.

Daga cikin sabbin alkalumman wadanda suka kamu da cutar, jihar legas ta na da mutane 19, sai Abuja mai mutane 9 Kano kuma na da mutane 5, sai mutane biyu daga jihar Oyo.

Cibiyar NCDC ta bayyana hakan ne a shafin ta na Twitter, tare da tabbatar da mutane 442 da suka kamu da cutar,  a Nijeriya, sai dai mutane 152 sun warke daga cutar yayin da mutane 13 sun mutu.

NCDC ta kuma bayyana alkalumman jihohin da cutar ta ratsa, inda jihar Lagos ke da mutane 251, Abuja  67, sai jihar Kano 21 jihar Osun mutane 20, Edo 15, jihar Oyo kuwa 13, Ogun ta na da 9, Katsina 7, sai jihohin Bauchida Kaduna da Akwa Ibom mutane shidda-shidda, jihohin Kwara da Delta hur-hudu, Ondo  3, jihohin Enugu da Ekiti da Rivers da Neja biyu-biyu, yayin da jihohin Benue da Anambra ke da guda-guda.

Leave a Reply