Home Labaru Abba Kyari: Tarihin Rayuwar Shugaban Ma’aikatan Buhari

Abba Kyari: Tarihin Rayuwar Shugaban Ma’aikatan Buhari

1570
0
Abba Kyari shi ne mutum mafi girman matsayi da cutar COVID-19 ta fara kawawa a Najeriya
An gano Abba Kyari ya kamu da cutar COVID-19 ne bayan dawowarsa Najeriya daga kasar waje.

Malam Abba Kyari na daga cikin kusoshin gwamanti masu fada a ji a gwamantin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Abba Kyari yana daga cikin mutum 17 da cutar COVID-19 ta kashe a Najeriya yayin da yawan wadanda suka kamu da ita a kasar ya karu zuwa 493.

Sau da dama ana zargin sa da juya akalar gwamnatin shugaban kasar, da kuma hana mata ruwa gudu.

Gwamnatin Shugaba Buhari ta sha yin watsi da zargin juya akalarta, sannan ta wanke shi daga zargin da ake masa na karbar rashawa.

Domin sanin wanene Malam Abba Kyari, mun yi waiwaye a kan tarihin rayuwarsa.

Asalin Abba Kyari

An haifi Abba Kyari, dan kabilar Kanuri ne, a jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya.

Iliminsa

  • Karatunsa na firamare da sakandare ya yi ne a jihar ta Borno.
  • Ya tafi kasar Ingila inda ya yi digirinsa na farko a fannin halayyar dan Adama (Sociologoy) a Jami’ar Warwick a shekarar 1980.
  • Abba Kyari ya kuma yi digiri a fannin Shari’a a Jami’ar Cambridge da ke a Ingilar
  • Ya zama lauya a 1983 bayan kammala makarantar koyar da aikin lauya ta Najeriya (Nigerian Law School).
  • Ya yi digiri na biyu a fannin Sharia’a wanda ya kammala a 1984 a A Jami’ar Cambridge.
  • A 1992 Abba Kyari ya yi Kwalejin Gudanarwa ta Lausanne da ke kasar Switzerland.
  • 1994 ya yi kwas din Gudanarwa da Ci Gaban al’umma a Makarantar Koyon Kasuwanci ta Harvard.

Ayyukan Abba Kyari

Ayyukan da Abba Kyari ya yi a tsawon rayuwarsa sun hada da:

  • Editan New Africa Holdings Limited Kaduna a 1988 – 1990.
  • A 1990, aka nada shi Kwamishinan Gandun Daji da Albarkatun Dabbobi na jihar Borno.
  • Ya kuma yi sakataren kwamitin gudanarwa na bankin African International Bank Limited.
  • Marigayin ya kuma yi darektaa a Bankin UBA.
  • Daba baya an nada shi a matsayin shugaban bankin.
  • A 2002, an nada shi a matsayin darakta a kaamfanin Unilever Nigeria.
  • Ya kuma yi aki a kamfanin mai na Exxon Mobil ne.
  • Ya bar duniyar a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasar Najeriya.

Matsayinsa a Fadar Gwamnati

Nada shi a mukamin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a shekarar 2015 ta sanya Abba Kyari a idanun jama’a, inda ake zargin mamacin da yana juya akalar gwamnati da kuma rashawa.

Matsayin ya ba shi damar fada a ji a kan kusan komai da ya shafi shugaban kasar. Ofishinsa na Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa ne ke tsara dukkan ayyukan shugaban kasar.

Makusanta a fadar gwamantin sun ce a kullum Abba Kyari kan gana da Shugaba Buhari akalla sau hudu a kullum.

Kazaliki ya kan karbi bakuncin akalla mutum 20 a ofishinsa. Cikinsu har da gwamnoni da ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati masu son ganin shugaban kasa.