Home Coronavirus Yadda Aka Binne Abba Kyari

Yadda Aka Binne Abba Kyari

908
0
An yi wa gawar Abba Kyari Salla daga cikin mota, saboda gudun yada coronavirus
An yi wa gawar Abba Kyari Salla daga cikin mota, saboda gudun yada coronavirus

An yi wa gawar Abba Kyari sallar jana’iza ba tare da an fito da ita daga mota ba domin kare mahalarta daga kamuwa da cutar coronavirus.

Kazalika an hana taron zaman makokin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasar Najeriya, wanda annobar COVID-19 ta yi ajalinsa.

An gudanar da sallar jana’izar mamacin ne a kebe a Fadar Shugaban Kasa, kafin a kai mamacin makwancinsa.

Motar da ta dauki gawar Marigayi Malam Abba Kyari

Gawar Marigayi Abba Kyari ta isa Abuja ne da safiyar Asabar bayan rasuwarsa a Legas inda ake jinyarsa bayan ya harbu da annobar.

Gabanin sallar gawar, Kakakin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wato Garba Shehu, ya ce za a yi sallar jana’izar ne a kebe, domin guje wa yada cutar, kamar yadda jami’an lafiya suka ba da shawara.

An dauki matakin ne da nufin kauce wa yaduwar cutar ta coronavirus ta dalilin taruwar jama’a a wurin sallar jana’izar.

Saboda haka a cewarsa babu zaman makoki kuma, “Ana bukatar ‘yan uwa da abokan arziiki da kuma sauran jama’a su yi masa addua’a.”