Home Labaru Kiwon Lafiya Covid-19: Mutane 23 Sunsake Kamuwa A Jihar Kano, Jimilla 59

Covid-19: Mutane 23 Sunsake Kamuwa A Jihar Kano, Jimilla 59

578
0
Covid-19: Mutane 23 Sunsake Kamuwa A Jihar Kano, Jimilla 59
Covid-19: Mutane 23 Sunsake Kamuwa A Jihar Kano, Jimilla 59

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta ce an samu karuwar mutane 23 da suka kamu cutar Coronavirus a Kano, wanda haka ya kawo adadin masu cutar 59 a jihar.

NCDC ta bayyana haka ne a cikin rahotan da ta fitar na daran ranar Litinin, game da halin da ake ciki  a kan Coronavirus a Nijeriya.

Cibiyar ta kara da cewa, samu karin mutane 38 da suka kamu da cutar a Nijeriya ya nuna jihar Legas ba ta samu wanda ya kamu da cutar ba.

Sanarwar ta kara da cewa, jihar Kano ce kan gaba a sabbin alkalumman masu cutar, sakamakon yadda ta ke da mutane 23, sai jihar Gombe da ke da mutum 5, Kaduna ta na da mutane uku, jihohin Borno da Abia na da mutane biyu-biyu, yayin da Abuja, Sokoto da Ekiti su ke da guda-guda.