Home Labaru Rikicin Afghanistan: Shugaba Biden Da Taliban Kowa Na Cewa Ya Yi Nasara

Rikicin Afghanistan: Shugaba Biden Da Taliban Kowa Na Cewa Ya Yi Nasara

48
0

Shugaba Joe Biden na Amurka ya kara kafewa kai da fata wajen kaare matakin da ya dauka na kawo karshen shekaru 20 da Amurka ke yaki a Afghanistan, da cewa bukata ta biya, ta kawar da Al Qaeda tun shekara goma baya.

Yayin da Taliban da ficewar sojojin Amurkar ta ba wa damar sake kama iko da kasar ke cewa ta yi galaba a kan Amurkar.

Duk da cewa ba wata manufa ba ce ta sauya a kan abin da Shugaba Biden din ya fada tun a baya game da ficewar sojojin Amurkar daga Afghanistan ba, matakin da ya bude kofa ga ‘yan Taliban suka koma suka sake damke mulkin kasar, wanda Amurkar ta jagoranci kwace wa daga wurinsu shekaru ashirin baya, abin da ya zamo tamkar hannun karba hannun bayarwa.

Sai dai a wannan karon shugaban ya jajirce kai da fata cewa matakin abu ne da ya kamata, domin Amurka a cewarsa ta riga ta samu biyan bukatarta tun da ta ga bayan kungiyar Al Qaeda tun shekara goma da ta wuce.