Home Labaru Zulum Ya Gana Da Shugaba Buhari

Zulum Ya Gana Da Shugaba Buhari

435
0
Zulum Ya Gana Da Shugaba Buhari
Zulum Ya Gana Da Shugaba Buhari

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi ganawar sirri da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar sa da ke Abuja.

Wata majiya daga tawagar gwamnan na cewa, tattaunawar ba ta rasa nasa ba da batun yakin da kungiyar Boko Haram a jihar  Borno da kuma kokarin da ake yi na maida ‘yan gudun hijira muhallin su.

Gwamnan dai ya shigo jirgi na musamman da ya yi daidai da umurnin fadar shugaban kasa kan rufe harkoki a Abuja saboda dakile yaduwar COVID-19 a Nijeriya.