Home Labaru Kiwon Lafiya Gwamnan Jihar Bauchi, Ya Warke Daga Coronavirus

Gwamnan Jihar Bauchi, Ya Warke Daga Coronavirus

307
0
Gwamnan Jihar Bauchi, Ya Warke Daga Coronavirus
Gwamnan Jihar Bauchi, Ya Warke Daga Coronavirus

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya bayyanawa duniya cewa ya warke daga cutar Coronavirus bayan gwaji na biyu da aka yi masa ya tabbatar bai dauke da cutar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a shafin sa na Tuwita da yammacin Alhamis 9 ga watan Afrilu, tare da yin Hamdala ga Allah Madaukakin Sarki.

Gwaji da aka yi wa gwamnan karo na biyu ya nuna cewa gwamnan ya warke, ina ya mika godiyar sag a daukacin al’ummar jihar bisa addu’o’i da nuna goyon baya da su nunawa gwamnatin a lokacin da ya killace kan sa.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 24 ga Maris ne gwamnan Bala Muhammed ya kamu da cutar Coronavirus.