Home Labaru An Kashe Mutane 2 Da Ke Yi Wa ‘Yan Bindiga Leken Asiri...

An Kashe Mutane 2 Da Ke Yi Wa ‘Yan Bindiga Leken Asiri A Katsina

516
0
An Kashe Mutane 2 Da Ke Yi Wa ‘Yan Bindiga Leken Asiri A Katsina
An Kashe Mutane 2 Da Ke Yi Wa ‘Yan Bindiga Leken Asiri A Katsina

Wasu mutane biyu da ke kaiwa masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga bayanan sirri a jihar Katsina sun gamu da ajalin su.

Mutanan wanda suka hada da Ibrahim Maye da Bishir Mai Laya ana ake zargin su ne da yi wa ‘yan bindiga leken asiri, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar su a karshen makon da ya gabata.

Wata majiya ta ce, an kashe mutanan ne a lokacin da su ke  kokarin sanar da masu garkuwa da mutane wani sako a kusa da dajin Kasuwar Gora da ke karamar hukumar Safana, wanda dukkanin su sun fito ne daga kauyen Hayin Gada a karamar hukumar Dutsinma.

Majiya ta kara da cewa, da isar mutanan dajin sai su ka hadu da wani tsohon dan leken asiri mai suna Amale, da ya tuba ba tare da sun sani ba, sai ya mika masu sunayen mutane uku da ya ke so yi garkuwa da su, matakin da ya bada damar kama su tare da fallasa asirin sauran ‘yan leken asirin.

Sai dai wata majiya daga jami’an ‘yan sanda ta ce. tuni an fara farautar sauran ‘yan leken asirin bakwai da aka ce suna aiki a kauyukan Dutsinma da Kagara, sannan kakakin ‘yan sandan jihar Gambo Isah ya yi alkawarin gudanar dai bincike a kan lamarin.