Home Labaru Ziyarar Amurka: Garkuwa Da Mutane A Nijeriya Siyasa Ce Kawai – Osinbajo

Ziyarar Amurka: Garkuwa Da Mutane A Nijeriya Siyasa Ce Kawai – Osinbajo

265
0
Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Kasa

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da ke zama a kasashen waje, su yi watsi da ce-ce-k-cen da ake yi cewa ayyukan garkuwa da mutane sun addabi mutanen Nijeriya.

Osinbajo ya bayyana haka ne yayin da ya ke tattaunawa da ‘yan Nijeriya a birnin New York na kasar Amurka, inda ya shaida masu cewa, abin duk siyasa ce kawai ba kamar yadda su ke ji a kafafen yada labarai ba.

Ya ce ana samun burbushin garkuwa da mutane jifa-jifa a Nijeriya, amma ba wannan ne farau ba, ya na mai cewa duk rahotanni da labarun da su ke ji a kafafen yada labarai cewa an yi garkuwa da mutane duk ba gaskiya ba ne siyasa ce kawai.

Osinbajo ya cigaba da cewa, a duk lokacin da aka kawo labarin an yi garkuwa da wani sai sun yi bincike sosai, amma daga karshe sai su gano ashe hira ce ta mutane ba gaskiya ba ce.

Ya ce gwamnati na iyakar kokarin ta wajen ganin an shawo ko kuma an kawo karshen matsalolin tsaro a Nijeriya, kamar yadda kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya ya wallafa.

Leave a Reply