Mai taimaka wa shugaban kasa ta fuskar yada labarai Femi Adesina, ya ce a wannan karo, shugaba Buhari ba zai dauki dogon lokaci wajen fitar da sunayen Ministocin sa ba.
Femi Adesina ya bayyana haka ne, yayin wata hira da ya yi da Mujallar Interview Magazine.
A shekara ta 2015 dai, shugaba Buhari ya dauki kusan rabin shekara ba tare da ya kafa gwamnati ba, lamarin da ya janyo jama’a su ka fara kiran sa ‘Baba Go Slow’.
Adesina, ya ce shi kan sa shugaba Buhari ya fada da bakin sa cewa, a wannan karon ba za a jima wajen kafa gwamnati kamar yadda a ka yi a shekara ta 2015 ba.
You must log in to post a comment.