Home Labaru Siyasar Zamfara: Kwamitin Bincike Ya Ce Yari Ya Yi Wa Kassara Naira...

Siyasar Zamfara: Kwamitin Bincike Ya Ce Yari Ya Yi Wa Kassara Naira Biliyan 250

477
0

Kwamitin Karbar Mulki da Bincike da Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya kafa, ya yi zargin cewa tsohon gwamnan jihar Abdul’aziz Yari ya hallaka akalla naira biliyan 250 da miliyan 900.

Bayanin hakan ya bayyana ne, bayan Shugaban Kwamitin kuma tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Ibrahim Wakkala ya mika rahoton binciken shi, inda ya ce kwamitin ya tantance yawan basussuka da tabargazar da gwamnatin da ta sauka kwanan nan ta tafka a karashin Abdul’aziz Yari.

Ya ce sun yi iyakar kokarin bincike, amma sun rasa inda zunzurutun kudade har naira biliyan 250 su ka shige.

Wakala ya kara da cewa, daga cikin kudaden, har da tulin bashin naira biliyan 115 da miliyan 190 da dubu 477 da 572, wadanda ba a kai ga biyan masu ayyukan kwangilolin da aka rubuta ana gudanarwa ba har 462, sannan akwai kudaden ma’aikatan da su ka bar aiki da yawan su ya kai naira biliyan 1 da miliyan 431 da dubu 645 da 305.

Sai dai Kakakin Yada Labarai na Abdul-Aziz Yari Ibrahim Dosara, ya ce babu gaskiya a cikin bayanan rahoton kwamitin.