Home Labaru Ziyarar Aiki: Shugaban Hukumar NIS Ya Zo Kaduna

Ziyarar Aiki: Shugaban Hukumar NIS Ya Zo Kaduna

349
0
Muhammad Babandede, Shugaban Hukumar Kula Da Harkokin Shige Da Fice Na Najeriya NIS
Muhammad Babandede, Shugaban Hukumar Kula Da Harkokin Shige Da Fice Na Najeriya NIS

Shugaban hukumar kula da harkokin shige da fice na Najeriya NIS Muhammad Babandede, ya kawo wata  ziyarar aiki ta yini daya zuwa ofishin hukumar dake Kaduna, a kokarin sa na tabbatar da dorewar nasarar da hukumar ke samu wajen zamanantar da ayyukan ta.

Yayin ziyarar, Muhammad Babandede, ya kuma ziyarci gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, a fadar gwamnatin jihar ta Sir Kashim Ibrahim dake Kaduna.

Ya yaba wa gwamna Nasiru El-Rufai bisa goyon bayan da yake ba hukumar sa a jihar da kuma samar da kyakkyawan yanayi na gudanar da aikace-aikacen ta wajen bunkasa hada-hadar kasuwanci a Kaduna da tabbatar da dorewar zaman lafiya.

A nashi bangaren, gwamna El-Rufai, ya taya Shugaban na NIS, murna kan dimbin ci gaban da ya samar a cikin shekara uku na shugabancin sa, da kuma kokarin da yake wajen kawo       sauye-sauye masu ma’ana a hukumar.