Home Labaru Kammala Aiki: Masari Ya Sallami Mahukunta Hukumar Kula Da Maniyyata Ta Jihar

Kammala Aiki: Masari Ya Sallami Mahukunta Hukumar Kula Da Maniyyata Ta Jihar

237
0
Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina
Aminu Bello Masari, Gwamnan Jihar Katsina

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya amince da rushe kwamitin gudanarwa na hukumar kula da walwalar maniyyata ta jihar ba tare da wani bata lokaci ba.

Masari, ya umurci shugaban hukumar Abu Rimi, da sauran ‘yan kwamitin su gaggauta mika harkokin hukumar ga jami’i mafi girma da zai cigaba da tafiyar da harkokin hukumar kafin a nada wani sabon shugaba da kuma kwamitin gudanarwar. Da yake godewa ‘yan kwamitin kan irin gudumuwar da suka bada wajen tafiyar da harkokin hukumar gwamna Masari, ya yi musu fatan alheri a rayuwar su a nan gaba.