Home Labaru Zargin Cin Hanci: Za A Gurfanar Da Yahya Jammeh Gaban Kotu

Zargin Cin Hanci: Za A Gurfanar Da Yahya Jammeh Gaban Kotu

461
0
Yahya Jammeh, Tohon Shugaban Kasar Gambia
Yahya Jammeh, Tohon Shugaban Kasar Gambia

Gwamnatin Gambia ta bayyana cewa za ta sa a gurfanar da tsohon Shugaban kasar Yahya Jammeh, a gaban kotu kan laifin cin hanci da rashawa, da sata da laifukan da suka shafi karya tattalin arziki.

Sanarwar ta zo ne a ranar Juma’a bayan hukumar da ke binciken Yahaya Jammeh, ta wallafa sakamakon ta kan tafiyar da tattalin arziki da hukumomi da kamfanoni a lokacin mulkin sa da ya shafe shekaru 22.

Ministan shari’ar Gambia Aboubacarr Tambadou, ya ce barnar da Jammeh, ya tafka a kasar ta yi mummunar illa, don haka zai bukaci ‘yan majalisa su samar da kudurin da zai gurfanar da shi gaban shari’a.

Wani bincike na daban da aka gudanar a farkon shekarar nan, ya ce ya samu Yahya Jammeh, da sace dala biliyan daya a lokacin mulkin sa.

Yahaya Jammeh, dai ya fice ne zuwa Equatorial Guinea, bayan dakarun kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka sun shiga Gambia da zummar tilasta masa mika mulki ga mutumin da ya lashe zaben kasar Adama Barrow.

Leave a Reply