Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta karyata rahotannin barkewar wata sabuwar cuta a kauyen Gundutse da ke karamar hukumar Kura.
Jami’in yada labarai na ma’aikatar, Ibrahim Abdullahi, a wata tattaunawa ta wayar tarho a jiya, ya ce mutane bakwai ne suka mutu a cikin al’ummar sakamakon tsananin zazzabin cizon sauro da taifod, ba wata sabuwar cuta ba.
Ya bayyana cewa, bayanan da aka samu daga bincike da sa ido na masana DSNR a karamar hukumar sun nuna cewa, sananniyar cuta ce wato zazzabin cizon sauro da taifod ce da ta bulla a cikin al’ummar a cikin watan Ramadan.
A halin da ake ciki, Abdullahi ya kara da cewa, gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki sun dauki matakan shawo kan lamarin yayin da ake ci gaba da sa ido.














































