Home Labaru Zargin ‘Yan Majalisa Da Sace Kayan Ofis: Sanata Oshiomhole Ya Bada Haƙuri

Zargin ‘Yan Majalisa Da Sace Kayan Ofis: Sanata Oshiomhole Ya Bada Haƙuri

48
0

Dan majalisar Dattawa Sanata Adam Oshiomhole, ya ba
Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai haƙuri, bayan ya zargi
waɗanda ba su zarce a zaɓen shekara ta 2023 ba da wawure
kayan ofisoshi lokacin da za su tafi.

Adam Oshiomhole ya yi zargin ne a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, inda ya bayyana yadda Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai su ka sace kayan ofisoshi, ciki kuwa har da tebura ba su bari ba.

A zaman majalisar na ranar Talatar da ta gabata, Sanata Solomon Adeola ya ce ya dace Oshiomhole ya bada haƙuri, kuma ba za a biya shi kuɗaɗen sallama ba har sai ya aikata hakan.

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio, ya ce wa Oshiomhole naira biliyan 70 da za a ba sanatoci da ‘yan majalisar wakilai ba tallafin shinkafa ba ne saye-sayen kayan ofisoshi za a yi da su.

Leave a Reply