Home Labaru Kotu Ta Tabbatar Da CONUA Da NAMDA A Matsayin Halastattun Kungiyoyin Kwadago

Kotu Ta Tabbatar Da CONUA Da NAMDA A Matsayin Halastattun Kungiyoyin Kwadago

43
0

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta sha kaye a kotu,
a yunkurin ta na ganin ta haramta kungiyoyin CONUA da
NAMDA da su ka kasance kishiyoyin ta.

Da ta ke yanke hukunci a kan shari’a tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU, Kotun masana’antu ta kasa ta tabbatar da CONUA da NAMDA a matsayin halastattun kungiyoyi masu cin gashin kan su, wadanda su ka yi rajista da kungiyoyin kwadago kuma su na da ‘yancin gudanar da ayyukan su a manyan makarantun Nijeriya.

Kungiyar ASUU dai ta yi karar Ministan kwadago da ayyuka da registra da kungiyoyin CONUA da NAMDA a matsayin wadanda ta ke tuhuma guda hudu.

Da ya ke gabatar da hukunci, mai shari’a Benedict Kanyip ya jaddada cewa, bisa dokokin kungiyar kwadago ta duniya, ya halasta a samu kungiyoyin kwadago sama da guda a ma’aikata guda.

Kotun ta ce, bukatun mai shigar da kara ba su yi nasara ba, kuma ba a mince da bukatun ba sannan wannan ita ce atsayar kotu.

Bisa shaidun da kotu ta tabbatar, mai kara ya shigar da karar ne ta asalin sammacin da ya shigar a ranar 26 ga watan Yuni na shekara ta 2022.

Leave a Reply