Home Labaru Juyin Mulki: ECOWAS Za Ta Tabbatar Da Dimokuradiyya A Nijar – Tinubu

Juyin Mulki: ECOWAS Za Ta Tabbatar Da Dimokuradiyya A Nijar – Tinubu

288
0

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya maida martani a kan
rikicin siyasar da ke kokarin kunno kai a Jamhuriyar Nijar,
inda ya bayyana goyon bayan sa ga zababbiyar gwamnatin
dimokuradiyya ta kasar.

Yayin da rikici a Jamhuriyar Nijar ke kara kunno kai, a madadin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, Tinubu ya jaddada aniyar sa ta tabbatar da dimokuradiyya da tsarin mulki a kasar.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa, za su tsaya tsayin daka wajen goyon bayan zababbiyar gwamnati a Nijar, ya na mai addada muhimmancin kiyaye dimokuradiyya ga al’ummar ijar da zaman lafiya da ci-gaban yankin yammacin Afirka baki daya.

Ya ce, bayanan da ke fitowa daga Jamhuriyar Nijar na nuni da cewa, wasu abubuwa marasa dadi su na faruwa a kan manyan shugabannin siyasar kasar, don haka ya kamata duk wadanda ke da hannu a lamarin sun san cewa shugabannin ECOWAS da duk masu kaunar dimokuradiyya a duniya ba za su goyi bayan lamarin ba.

Ya ce a matsayin shi na shugaban kungiyar ECOWAS, ya na
jadadda aniyar goyon bayan Nijeriya ga zababbiyar gwamnati
a Nijar, sannan ya tabbatar da cewar shugabannin ECOWAS

Leave a Reply