Home Labaru Zargin Wuru-Wuru: An Fara Shari’ar Tsohon Kwamanda Manjo Janaral Hakeem Otiki

Zargin Wuru-Wuru: An Fara Shari’ar Tsohon Kwamanda Manjo Janaral Hakeem Otiki

284
0

An kaddamar da shari’ar musamman game da tsohon Kwamandan Rundunar Sojin Nijeriya da ke jihar Sokoto Manjo Janaral Hakeem Otiki, bisa ga Sashe Na 8 a kan zargin karkatar da makudan kudaden da su ka kai miliyoyin Nairori.

Shari’ar, wadda aka fara a babbar kotun soji da ke ofishin Jami’an Sojoji a Abuja, an fara ta ne da misalin karfe 12:30 na yammacin ranar Talatar da ta gabata.

Babban Hafsan Soji ne ke jagorantar shari’ar, a karkashin jagorancin Shugaban Rundunar Tsaro da Tsare-Tsare ta helkwatar sojojin Nijeriya Laftanar Janar Lamidi Adeosun, wanda shi ne kuma Alkalin kotun soji na musamman.

An dai tabbatar da cewa, an kama sojoji biyar da su ka yi batan-dabo a kan hanyar Sokoto zuwa Kaduna, yayin da aka aike su da kudin a makon farko na watan Yuli na shekara ta 2019.

Alkalin kotun Laftanar Janar Lamidi Adeosun, ya ce kotun ta samu hurumin yin shari’ar ne bisa ga sashe na 131, karamin sashe na 101 na Dokokin Soji da ke cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya, ya na mai bada tabbacin cewa, kotun za ta yi gaskiya da adalci yayin gudanar da shari’ar.