Home Labaru Tattalin Arziki: Za Mu Iya Wadata Nijeriya Da Madara Ba Sai An...

Tattalin Arziki: Za Mu Iya Wadata Nijeriya Da Madara Ba Sai An Shigo Da Ita Ba – Miyetti-Allah

175
0

Sakataren Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Othman Ngelzarma, ya ce yawan makiyayan da ke Nijeriya sun isa a ce kasar nan ta na cike da wadatar madara ba sai an rika shigowa da ita daga kasashen waje ba.

Ngelzarma ya bayyana haka ne, yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Abuja, inda ya ce yanzu haka ya na tabbatar da cewa akwai akalla shanu miliyan 70 da ake kiwo a fadin Nijeriya, sai dai babbar matsalar da ake samu it ace, babu kamfanonin sarrafa madarar shanun ko da an fiddo ta daga rugage.

Ya ce babu wuraren da Fulani za su rika kai nono a na saye domin sarrafa shi.

Ngelzarma ya kara da cewa, za a samar da wuraren saida nonon shanu idan aka tatso.

A karshe ya yi kira ga gwamnatin tarayya da jihohi su kafa kamfanoni domin makiyaya su rika saida nono a wani mataki na bunkasa tattalin arzikin kasa.