Home Labaru Korafin Zabe: Kotun Zabe Ta Yi Watsi Da Karar Da PDP Ta...

Korafin Zabe: Kotun Zabe Ta Yi Watsi Da Karar Da PDP Ta Shigar A Jihar Neja

190
0

Kotun kararrakin zaben gwamna a jihar Neja, ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takarar ta Umar Nasko su ka shigar a kan Gwamna Abubakar Bello na jam’iyyar APC.

Jam’iyyar PDP da dan takarar ta dai su na kalubalantar nasarar Abubakar Bello a zaben gwamna da aka gudanar, cewa gwamnan ya gabatar wa hukumar zabe takardun shaidar karatu na bogi.  

Mai shari’a John Igboji na kotun zaben, ya ce ba zai iya tozarta tsarin kotu ba, saboda wata babbar kotun tarayya ta riga ta saurari karar kuma ta yanke hukunci.

Haka kuma, kotun ta amincewa da karar da aka shigar a kan APC da Umar Nasko, bisa zargin Gwamna Abubakar Bello da mallakar takardun karatu na bogi.