Home Labaru Zargin Rashawa: Za A Cigaba Da Shari’ar Fayose Da EFCC Ranar ...

Zargin Rashawa: Za A Cigaba Da Shari’ar Fayose Da EFCC Ranar 21 Ga Watan Oktoba

182
0

Rahotanni na cewa, shari’ar da ake yi da tsohon gwamman jihar Ekiti Aydole Fayose za ta cigaba a Ranar 21 ga Watan Oktoba na shekara ta 2019.

Ana dai shari’ar ne a babbar kotun tarayya da ke Legas, inda Hukumar EFCC ta ke zargin Fayose da wawurar Naira biliyan 6 da miliyan 900 daga asusun jihar Ekiti a lokacin ya na gwamna.

A cikin watan Oktoba na shekara ta 2018 ne, hukumar EFCC ta fara gurfanar da Fayose a gaban mai shari’a Mojisola Olatotegun na babbar kotun tarayya da ke Legas.

EFCC ta tuhumi tsohon gwamnan da laifuffuka 11, wadanda su ka hada da sata da karkatar da kudade, sannan daga baya an sake gurfanar da shi a gaban mai shari’a Chukwujekwu Aneke a shekara ta 2019.

Sai dai Fayose ya karyata zargin da ke wuyan sa, lamarin da ya sa aka nemi a bada belin sa da sunan zuwa asibiti a kasar waje domin a duba lafiyar sa.