Home Labaru Kyamar Baki: Ba Za Mu Kai Karar Afirka Ta Kudu Ga Majalisar...

Kyamar Baki: Ba Za Mu Kai Karar Afirka Ta Kudu Ga Majalisar Dinkin Duniya Ba – FG

250
0
Geoffrey Onyeama, Ministan Harkokin Wajen Nijeriya
Geoffrey Onyeama, Ministan Harkokin Wajen Nijeriya

Ministan harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama, ya ce gwamnatin Nijeriya ba za ta kai karar kasar Afirka ta kudu ga majalisar dinkin duniya a kan cin zarafin iyan Najeriya a wajen taron gangamin da zai gudana a a birnin New York na kasar Amurka.

Geoffrey Onyeama ya kara da cewa, ana tattaunawar difilomasiyya don ganin yadda za a biya ‘yan Nijeriyar da abin ya shafa wasu kudade.

Idan dai za a iya tunawa, shugaba Buhari ya amince da hakurin shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, a kan hare-haren da aka kai wa ‘yan Nijeriya a kasar sa.

Shugaba Buhari, wanda ya siffanta hare-haren a matsayin abin takaici, ya ce duk da haka za a cigaba da karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.

Buhari ya kuma tuna wa wakilan shugaba Ramaphosa irin gudunmuwar da Nijeriya ta bai kasar Afirka ta kudu saboda yawancin matasan kasar sun jahilci tarihi.