Home Labaru Zargin Rashawa: Babu Bi-Ta-Da-Kulli A Tsare Kanar Sambo Dasuki – Malami

Zargin Rashawa: Babu Bi-Ta-Da-Kulli A Tsare Kanar Sambo Dasuki – Malami

282
0
Zargin Rashawa: Babu Bi-Ta-Da-Kulli A Tsare Kanar Sambo Dasuki - Malami
Zargin Rashawa: Babu Bi-Ta-Da-Kulli A Tsare Kanar Sambo Dasuki - Malami

Ministan shari’a Abubakar Malami, ya musunta zargin cewa gwamnati na yi wa Kanar Sambo Dasuki bi-ta-da-kulli, ya na mai cewa kotu ta tabbatar da zargi a kan sa, kuma ta yi ma shi shari’a kamar yanda ta ke yi wa kowa.

Abubakar Malami, ya ce, maganar bi-ta-da-kulli ba ta taso ba, domin ana tuhumar Sambo Dasuki da laifi mai karfi, kuma wajibi ne a saurari bahasi daga gare shi.

Ya ce inda babu zargin aikata laifi a kan Dasuki ana iya cewa an yi ma shi bi-ta-da-kulli.

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a kan zargin da ake yi wa gwamnati na yin biris da laifuffukan wasu jami’an tsohuwar gwamnati amma ta kama Dasuki saboda ya taba kama shugaba Buhari a shekarun baya, ministan ya ce wannan gwamnati ta gurfanar da duk wanda aka samu da aikata laifi a gaban kotu kafin a ba shi beli.