Home Labaru Shugabanci: Ina Fatan Tarihi Zai Yi Min Adalci – Buhari

Shugabanci: Ina Fatan Tarihi Zai Yi Min Adalci – Buhari

288
0
Shugabanci: Ina Fatan Tarihi Zai Yi Min Adalci - Buhari
Shugabanci: Ina Fatan Tarihi Zai Yi Min Adalci - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ya na taka-tsan-tsan da aikin sa a matsayin Shugaban kasa, domin tunda aka rantsar da shi bisa ka’idar kundin tsarin mulkin Nijeriya, da izinin Allah zai bi tsarin yadda ya kamata har zuwa karshen wa’adin mulkin shi.

Yayin da ya karbi bakuncin tawagar mazauna birnin Abuja bisa jagorancin ministan Abuja Mohammed Bello da su ka kai ma shi ziyarar Kirisimeti a fadar shi da ke Abuja, Buhari ya ce ya na fatan tarihi zai yi ma shi adalci da ‘yan Najeriya.

Shugaba Buhari, ya ce ayyukan tsagerun yankin Neja Delta ne su ka kara tabarbarar da rashin ababen more rayuwa da gwamnatin sa ta gada, sai dai ya ce a shekaru hudu da su ka gabata, gwamnatin tarayya ta samu ci-gaba wajen hada albarkatun kasa domin sake gina ababen more rayuwa a fadin Nijeriya.

Buhari ya bayyana shekara ta 2019 a matsayin mai tarin nasara ga Nijeriya, inda ya yi godiya ga ‘yan Najeriya bisa imanin da su ka yi da shi, da kuma mara wa gwamnatin sa baya wajen kai Nijeriya zuwa mataki na gaba.