Home Labaru Baba Go-Slow: Duk Sunan Da Za Ku Kira Ni Da Shi Baya...

Baba Go-Slow: Duk Sunan Da Za Ku Kira Ni Da Shi Baya Damu Na – Buhari

602
0
Baba Go-Slow: Duk Sunan Da Za Ku Kira Ni Da Shi Baya Damu Na - Buhari
Baba Go-Slow: Duk Sunan Da Za Ku Kira Ni Da Shi Baya Damu Na - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce duk abin da za a fada game da shi ko kuma sunan da za a kira shi hakan ba zai sanya shi damuwa ba, domin ba zai fasa riko da kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekara ta 1999 ba.

Buhari ya karbi bakuncin mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo kafin ziyarar tawagar mazauna birnin Abuja, inda Osinbajo ya mika ma shi katin gaisuwar Kirismeti da wasu kyaututtuka.

Da ya ke bayyana godiyar sa ga Osinbajo, Buhari ya ce gwamnatin sa za ta maida hankali wajen samar da ababen more rayuwa ga ‘yan Najeriya, musamman tituna da lantarki da layin dogo ba tare da la’akari da maganganun masu magana ba.

Ya ce idan ka sama wa ‘yan Nijeriya manyan ababen more rayuwa an gama da su, domin kowa zai yi harkar gaban sa ne ba za su taba damuwa da wanene a gwamnati ba.

Shugaba Buhari, ya jaddada godiyar sa ga ‘yan Nijeriya da su ka sake zaben sa karo na biyu, inda ya ce ya na sane da cewa mafi yawan mutanen da su ka zabe shi ba su zabe shi don kudi ba, don haka ya ce ba zai yi kasa a gwiwa wajen bauta wa Nijeriya ba.