Home Labaru Zargin Kisan Gilla: An Kama ‘Yan Sandan Da Suka Kashe Wasu Matasa...

Zargin Kisan Gilla: An Kama ‘Yan Sandan Da Suka Kashe Wasu Matasa A Kano

82
0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu jami’anta da ake zargi da kisan wasu matasa a karshen mako.

Wasu iyayen matasa sun shiga ɗimauta da rokon a bi kadin rayukan ƴaƴansu da ake zargin ƴan sanda da hallaka su.

Lamarin ya janyo tunzuri inda matasa suka yi kone-konen tayoyi a unguwar Sharaɗa da ke cikin birnin Kano.

Wannan yanayi da iyayen matasan suka tsinci kan su na zuwa ne makonni da gudanar da gagarumar zanga-zanga kan cin zalin da ƴan sanda ke aikatawa a fadin ƙasar nan, lamarin da daga karshe ya juye zuwa tarzoma.