Home Labaru Gargadi: Ba Zan Sake Lamuntar Irin Zanga-Zangar #Endsars Ba — Buhari

Gargadi: Ba Zan Sake Lamuntar Irin Zanga-Zangar #Endsars Ba — Buhari

160
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ba zai sake bari zanga-zanga irin ta #EndSARS ta maimata kan ta a Nijeriya ba.

Yayin ganawar da ya yi majalisar da tsaro ta kasa, Buhari ya ce za a dama da masu ruwa da tsaki da matasa wajen kiyaye aukuwar irin ta nan gaba.

Ministan harkokin ‘yan sanda Muhammad Dingyadi ya bayyana wa manema labarai haka a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ya ce shugaba Buhari ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, zai yi duk abin da zai yiwu domin tabbatar da zanga-zangar EndSARS ba ta maimaita kanta a Nijeriya ba.

Shugaba Buhari ya kuma tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa za a dama da kowa, musamman matasa da sarakunan gargajiya da ma’aikatan gwamnati da malaman addini wajen tabbatar da zaman lafiya.