Home Labaru Kaduna: Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace Jiya A...

Kaduna: Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutum 9 Da Aka Sace Jiya A Hanyar Abuja

151
0
Yadda Jami’an Tsaro Su Ka Rutsa ‘Yan Fashi A Wani Banki Da Ke Abuja

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce sojojin da ke aikin tsaro na cikin gida sun ceto mutane 9 da aka yi garkuwa da su a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana haka ne  a cikin wata sanarwa, cewa ta karbi bayanan sirri daga Babban Ofishin tsaro na Operation Thunder Strike (OPTS) bayan abinda ya faru, da kuma tambayoyin mutane akan yadda ake ciki game da lamarin.

Sojojin dake sintiri na yau da kullun kan hanyar Akilubu-Gidan Busa akan hanyar Kaduna zuwa Abuja, sun sami kiran gaugawa da misalin karfe 4 na yamma, ce wa ‘yan fashi sun tare babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

‘Yan bindigar da ke dauke da makamai sun bude wuta a kan wata motar bas, dole ta sa direban ya tsaya. Lokacin da suka isa wurin, yan fashin sun riga sun sace mutane tara daga motar bas mai kujeru 18.